James 3

Kamewa Harshe

1Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai, ʼyanʼuwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shariʼa mafi tsanani. 2Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya kame dukan jikinsa.

3Saʼad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya. 4Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so. 5Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta mana. 6Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

7Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, 8amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da ɗafi mai kisa.

9Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke laʼantar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah. 10Daga wannan baki guda yabo da laʼana suke fitowa. ʼYanʼuwana, wannan bai kamata yǎ zama haka ba. 11Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya? 12ʼYanʼuwana, itacen ɓaure yana iya haifar ʼyaʼyan zaitun, ko kuma itacen inabi yǎ haifi ʼyaʼyan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.

Hikima Iri Biyu

13Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yǎ nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawaliʼun da suke fitowa daga hikima. 14Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

17Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; saʼan nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

Copyright information for HauSRK